23 Janairu 2018 - 10:39
Matsa miliyan 16 ne a Najeriya  basu da aikin yi

Wani Rahoto da hukumar kididdiga ta NBS a Najeriya ta fitar na watannin 4 karshen shekara ta 2017 ya ce ‘yan kasar miliyan 16 na fama da rashin aikinyi

Rahotan ya ce a cikin wadanan alkalluma mutane miliyan 8.5 na hada-hada cikin akalla sa’a guda domin samun abin kai wa baki, yayin da miliyan 7.5 ke zaman kashe wando.

Kazalika, akwai mutane miliyan 18.02 da ke aikin kasa da abin da ake bukata a mako wato sa’o’i 20 zuwa 39 maimakon sa’o’i 40.

Cikakkun Ma’aikata, da ke aikin Sa’o’i 40 zuwa sama da haka a watannin 4 farkon shekera ta 2018 sun kai miliyan 51.06, hakan ya sa ake da adadin Mutane miliyan 77.6 da ke da ayyukan yi a cewar NBS.

Sai dai kuma rahotan hukumar ya ce cikin mutane miliyan 77.6, miliyan 29.66 na ayyukan dogaro-da-kai da ya danganci noma, yayin da miliyan 21.66 sun dogaro ne ba ta hanyar noma ba.

Akwai kuma mutane miliyan 19.72 da albashinsu ya dogara a kan yawan aikin da sukayi a ranar, wadda su ne kashi 25.42 na yawan ma’aikatan da ake dasu a watannin 4 karshen shekara ta 2017.

Masu aiki gida da shago da wadanda ba’a biyansu sun kai kashi 7.30 da kashi 1.11 na adadin ma’aikata da ake da su.

Rahotan ya kuma bayyana cewa maza sunfi mata aikin cikakken lokaci, inda alkalluma mafi yawa na mata ke aiki gajeren lokaci tsakanin sa’o’i 20 zuwa 39 wasu ma kasa da sa’o’i 20 a mako.

Alkalluman maza da ke aikin cikakken lokaci ya kai miliyan 34.85 adadin da ya rubanya na mata sau biyu a watannin 4 karshe a cikin shekara ta 2017.

Rahotan ya ce fanin Noma shi ya fi diban ma’aikata da kuma dogara-da-kai